_Buhari Ya Bijirewa Umarnin Majalisar Wakilai Akan Shirin Ɗaukar Ma'ikata 774, 000 a Faɗin Najeriya.

Shugaban Ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi fatali da umarnin Majalisar Wakilan Najeriya na dakatar da shirin Special Public Work.
Facebook/Muhammadu Buhari

Wanda Gwamnatin tasa ta shirya za ta ɗauki ma'aikata dubu ɗari bakwai da saba'in da hudu (774, 000) a faɗin ƙasar Najeriya.

Kowacce ƙamar hukuma ta Najeriya za ta samu mutum dubu daya (1000) wanda za su na karɓar albashin Naira dubu Ashirin (20k) duk ƙarshen wata na tsawon watanni 3.

Yau talata (5-1-2021) Shugaba Buhari ya bada umarnin kowacce Jiha ta ƙaddamar da shirin na Special Public Works.

Sai dai yan majalisar wakilan na zargin Shugaban na kulla wata maƙarƙashiya ce wacce za ya yi kamfen da ita na shekarar 2023.

Har-ila-yau har yanzu Shugaban bai aiyana wanda zai maye gurbinsa ba a Jam'iyyar APC.

Sai dai Majalissar Wakilai na zargi Shugaba Buhari na son wasan kura da hankalin ƴan Najeriya ne wajen kamfen kamar yadda ya yi da Trader Monie a shekarar 2019.

Biyo mu domin sanin wuraren da ake zuwa a nemi wannan aiki, sannan da takardun da ake so.

Post a Comment

Previous Post Next Post