A cikin wannan rubutaccen post za ka samu cikaken bayani akan shafin Top Hausa Novels, wadanda suke tafiyar da shi, wanda ya kirkireshi da kuma manufofin kirkirar sa.

THN ya samo asali ne daga abbreviation din Top Hausa Novels, ma'ana na anyi zuzzurfan tunani wajen ganin an takaita tsayin sunan shafin zuwa kalmomi uku, kuma yana amfani da domain extension din .com.ng.

Matashin da ya kirkira, zanawa kuma yake tafiyar da shafin sunansa Abba Abdullahi Garba ma'ana mutumin da ke tafiyar da shafin Abba Blog.

Hakikanin gaskiya aikinsa ya dan bada matsala da farko, to amma bayan na yi amfani da shawarwari daban-daban daga mutane daban-daban kamar irin su Shuraih Usman mai shafin DL-HAUSANOVELS da sauransu a karshe THN ya cimma ga ci.

Hoton da ke kasa, shine tambarin shafin Top Hausa Novels, kuma ko ina ka shiga za ka ga hotuna masu dauke da sunan shafinmu.

Kana son karanta karashen bayani akan wannan shafi na dauko cikakkun littafan hausa? To ci gaba da karanta wannan rubutu.

Manufar Bude Shafin THN

Tun wajen 2016 nake da sha'awar karatun littafan hausa, kuma nake son bada tawa gudunmawar wajen ganin na saukakawa masu karatun novels.

Ina da masaniya mafiya yawancin masu karatu da littafan hausa musamman na soyayya mata ne. Kuma masu son karatun littafan yaki maza ne mafiya yawancinsu

Amma wannan ba shine matsala ta ba, domin ko littafin waye, indai ka bida za mu siyeshi mu dorashi a shafinmu domin farin cikin maziyartansa. Har-ila-yau in har kai marubuci ne, kana son dora littafinka a shafin THN, kofa a bude take.

Baya ga haka, nan gaba kadan za mu fara dora cikakkun audio a shafin namu domin masu son sauraron hausa novels a audio. Sannan ba da jimawa ba za mu fara saka litattafai na addini, karatu da sauran fannin ilimummuka da dama a harshen hausa.

Wacce Irin Nasara Muke Son Cimmawa

Nasarar da muke son cimmawa dai ba wata gagaruma mace, muna yin iyaka kokarinmu wajen ganin mun zamo abin kwatance a cikin dukkanin shafukan hausa novels da ke arewacin Najeriya. 

Yanzu dai har yanzu shafin rarrafe yake, amma muna da yakinin nan da shekaru 2 zai kama kasa, ya fara gwara kan duk wadanda ba za su iya competing da mu ba. 

Rubutun kada ya yi tsayi. Mu dai fatanmu Allah ya bamu tsawon rai da nisan kwana domin ganin wannan dan tatsitsin mafarki ya cika.

Allahumma Ameen.

Post a Comment

Previous Post Next Post