Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, yau talata yace jam'iyyar APC ta samar da cigaba sama da wanda  PDP ta samar a tsawon shekaru 16 zamanin mulkinta.

Facebook/Gov Yahaya Bello

"A dunkule, APC ta ci nasarori sama da wadda PDP taci a tsawon zamanin mulkinta na shekaru 16 a Najeriya". 

Bellon ya fadi haka daga gidan gwamnatin Jihar Kogi dake Lakwaja.

Bello, ya fadi haka ne a hirarsa da, Channels Television cikin shirinsu na gari ya waye, yace, jam'iyyarsa tayi mulki nagartacce ma 'yan Najeriya.

"Nasarorin da APC ta samu cikin shekaru 6 sunfi wadda PDP ta samu yayin da ta mulki kasar na shekaru 16. Bayanan kididdiga na nan, kuma za mu tunatar da yan Najeriya a yanayin da APC ta gaji Najeriya, kuma a ina muke yau."

Tun bayan dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999, PDP ke rike da ragamar mulkin kasar har zuwa 2015, yayin da APC ta karbe mulkin kasar.

Shi kuwa dan takar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari ya lashi takobin magance matsaloli uku (tsaro, tattalin arziki sai cin hanci da rashawa) dake cin dunduniyar kasar muddin ya hau mulki.

Bayan wannan sako na yin maganin matsalolin Najeriya shekaru shida da suka gabata, Yan Najeriya suka taru kwai-da-kwarkwatarsu wajen dangwalawa jam'iyyar APC da zummar abubuwa za su sauya.

Gwamnan ya kuma yi magana akan tabarbarewar tsaro a kasar, ya yi kira ga yan Najeriya da su hadai kai wajen magance matsalar madadin siyasantar da matsalar tsaron.

Ya kuma bayyana cewa, fashi-da-makami ita ce babbar matsalar data addabi Najeriya kafin APC ta karbi ragamar mulkin kasar. Yahaya Bello yace jam'iyyarsa na iya kokarinta wajen magance aiyukan fashi-da-makami a fadin kasar.

Bangaren matsayin tsaron Jihar Kogi, Gwamnan ya maimaita yadda gwamnatinsa ta bada goyon baya wajen zakulo masu aikata laifuka.

Kamar yadda yace, Jihar Kogi ta kasance jiha mafi lafiya ta fannin tsaro, duk da harin 'yan ta'adda wadda ya jawo mutuwar kwamishina da kuma kwace ikon kamar hukuma guda da 'yan ta'adda suka yi.

Yace, "Na fada na kara Jihar Kogi ita ce jiha mafi zaman lafiya a Najeriya. Hakan ba yana nufin babu wasu matsaloli da muke fama da su bane."

"Kamar yadda nasha fada, za su zo da yawansu, amma ba za su taba komawa ba, musamman yan ta'addan. Eh akwai wurare da suka yi kaurin suna a jihar."

Post a Comment

Previous Post Next Post