Tsohon shugaban riko na hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu,
an Kara mashi girma zuwa matsayin Mataimakin Sufeto-Janar (AIG) a wannan makon daga Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda (PSC)

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa kwamitin sauraron shari’ar Ayo Salami ne ya ba da shawarar cire Magu, wanda aka kara wa mukamin zuwa kwamishinan ‘yan sanda a shekarar 2018, wanda kuma ya nemi a gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin yin amfani da ofis.

Kwamitin ya ba da shawarar musamman cewa a cire Magu “saboda rashin yin lissafin N431,000,000.00 na asusun bayanai da aka saki zuwa ofishin Shugaban Hukumar na EFCC tsakanin watan Nuwamba na 2015 Zuwa Mayu
2020.

Post a Comment

Previous Post Next Post